Daga Ahmad N. Argungu
Marigayi Kangiwa wanda ya rasu 17 ga nuwanba 1981 ya yi aiki a matsayinsa na gwanna ne duka natsawon shekaru biyu da wata daya da kwanaki goma sha shida, amma cikin dan wannan kankanen lokaci babu fannin da gwannatinsa ba ta taba ba wajen aiwatar da ayukkan cigaban jiharsa.
A lokacin rayuwarsa, wasu na yi wa Shehu Kangiwa kallon mutum mai basira, da hange nesa da kyauta da yin haba-haba da jama’arsa. Kwarjininsa ya kara fice tare da karuwa wajen jiharsa lokaci taron gwannonin Jam’iyar NPN. A fagen siyasa kuma takwarorinsa na kallonsa a matsayin mai dinbin hikimomi da dabarun shawo kan magoya baya musaman a fagen kanfe. Mutum ne mai sha’awar wasanin motsa jiki kamar kwallon dawaki wato Polo wadda shi ne sanadiyyar kafuwarta a Sokoto. Da yawa daga cikin abokansa na kallonsa mutum mai kwazo da cika alkawali. Shahararen Mawakin na Hausa Alhaji Sani Aliyu Dan dawo wanda shi shi ma Allah ya yi masa cikawa ya kan kira shi “Shehu mai fada da cikawa ne” akidar da aka rasa a wajen siyasar wannan lokaci da muke ciki.
Lokaci da aka kawo gawar marigayi Kangiwa zuwa Sokoto daga Kaduna, fiye da jiragen sama 25 ne suka sauka a filin saukar jiragen sama na Sokoto dauke da dubban mutane masoyansa da abokansa da ‘yan siyasa daga ciki da wajen Nijeriya domin su halarci jana’izarsa. Wannan ya nuna irin kyakkyawan zaman da Shehu Kangiwa ya yi da jama’a a ciki da wajen Nijeriya.
Alhaji Isa Kangiwa (Mutawallen Argungu) shima Allah ya wa rasuwa cikin shekara (2018) wanda shi ne Kwamishinan gidaje da muhalli lokacin gwannati Shehu Kangiwa wanda kuma ajinsu daya tun suna yara ya bayyana marigayi Kangiwa da cewa “mutum wanda ya fi kowa basira a cikin ajinsu tun suna yara.”
Lokacin rayuwanrsa, Marigayi Shehu Kangiwa ya samu nasarori da dama a rayuwarsa. A fagen ilmi jihar Sokoto wanda ta hada da jihar Kebbi da jihar Zamfara a yau duk sun shedi bude makarantu da daga darajjojin wasu zuwa manyan makarantu. Sannan yawan dalibai masu shiga makarantu sun karu, baya ga samuwar ingantuwar yanayin koyarwa da yanayi karatu ga malamai da kuma dalibai. Lokacin gwannati Shehu Kangiwa a fito da shirin gine-ginen gidajen ma’aikata da otal-otal da ofis-ofis inda aka gina Giginya Sakariya (Shehu Kangiwa Sakatariya) da gidajen Kwamishinoni na titin Sama da gidajen ma’aikata na Unguwar Bado. Sai Giginya Otal da kuma Shukura. Lokacinsa ne a aka gina gidan tarihin mai suna Wazirin Junaidu History Bureau, da kuma dakin karatu watau State Library wanda ke titin Sultan Abubakar Sokoto da sauransu. Gwannatin Kangiwa ta samar da hanyoyi mota manya da kanana da suka hada babban birnin jihar da sauran sassan manyan garuruwan da kauyukka.
Ana iya samun Ahmad N. Argungu ta Adareshinsa na yanar gizo tanimunanabo@gmail.com
