Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana jin dadinsa game da sauya sheƙar Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas.
Shettima ya ce sauya shekar Kefas zuwa jam’iyyar APC a matsayin abin alfahari da ya taba zuciyarsa ƙwarai.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a Jalingo, babban birnin Taraba, yayin bikin tarba na musamman da aka shirya domin maraba da gwamnan cikin jam’iyya mai mulki, cewar Vanguard.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya nuna fata cewa gwamnoni a jihohin Adamawa da Bauchi za su sake duba matsayinsu su mara wa APC baya.
A wajen taron, Shettima ya ayyana Gwamna Kefas a matsayin jagoran APC a Taraba, tare da kiran mambobin jam’iyyar su mara masa baya.
Ya ce goyon bayan jam’iyya zai ƙarfafa gwamnan wajen haɗa kan al’ummar jihar da kuma samar da ribar dimokuraɗiyya ga jama’a.






