Tsawon shekara guda ana fafata shari’a kan gida da yake saman hanyar Waziri Macciɗo a unguwar Bazza cikin birnin sokoto, wani abu da ya yi kama da wasan kwaikwayo a ranar Assabar data gabata waƙillan kotu tare da jami’an tsaro sun yi nasarar zartar da umarnin kotu wanda ta bayar kan Hajiya Balkisu Ibrahim Bazza da ta tashi a gidan da take zaune a ciki.
Fitar da ita da aka yi gidan ya faru ne bayan samun nasarar hukuncin ƙarshe da kotun kula da hayar gidaje ta yi kan ƙarar da aka shigar gabanta mai namba SSRT/116/2025, wadda Alhaji Junaidu Usman Junaidu ya kai kokensa kan gida mallakinsa ne, wadda ke ciki ta kasa martaba doka.
Tun farko gidan Honarabul Umar Bature ya gade shi ga babansa, ya sayar da shi ga Alhaji Ya’u Umar, shi kuma baya zama Sokoto sai ya bar surukarsa Hajiya Balkisu ta koma gidan da zama, sai ya gyara daki a gidan wanda yake amfani da shi duk sanda bukatar hakan ta taso.
Dangantar surukan ta lalace ne bayan da Alhaji Ya’u ya yanke shawarar sayar da gidan ga Alhaji Junaidu Usman Junaidu. Bayan Junaidu ya sayi gidan lauyansa Umar Aminu ya sanar ya aika takarda ga Hajiya Balkisu a bukatar da ake da ita na ta tashi ta bayar da gida kan haka an ba ta kwana bakwai, tun 9 ga watan Maris na 2025 aka sanar da ita.
Da Balkisu ta ƙi tashi gidan sai lauyoyin Junaidu suka koma gaban kotun mai kula da bayar da hayar gidaje suna buƙatar umarnin zartar da hukunci, a 24 ga watan Mayu 2025.
Ana haka ne sai Hajiya Balkisu ta sanya ƙararraki a gaban kotun shari’a domin ta ƙwato gidan.
A farko ta shigar da ƙara mai mamba CV/083/2025, ta neman kotu ta tabbata da Alhaji Ya’u A. Umar shi ne ya ba ta kyautar gidan(Hiba), bayan da kotu ba ta samu hujjoji gamsassu ba ta yi watsi da ƙarar.
A karo na biyu ta sake sanya sabuwar ƙara a kotun Shari’a(CV/153/2025) waton (Hajiya Balkisu Ibrahim Bazza Vs. Alh Ya’u A. Umar), a wannan karon ta nuna Alhaji Ya’u ne ya ba ta kyautar kuɗi ta yi amfani da su ta sayi gidan, tana son kutu ta tabbatar mata da hakan, ita ma wannan ƙarar an yi watsi da ita.
Bayan kammala shari’ar ciyaman na kotun bayar da hayar gidaje ya bayar da umarnin ƙarshe na a tayar da su a 22 ga watan Mayu 2026 saboda ta saɓawa umarninsa, washe gari 23 ga watan aka zartar da hukunci.
A cewar shaidun gani da ido a wajen kotu Buhari Umar Bazza, ana ƙoƙarin zartar da hukuncin ne sai lamarin ya zama wani abu daban, saboda ana aikin ne lauya A. M. Jariri ya zo wurin, jami’an kotu suka yi masa bayani kan halin da ake ciki tare da gabatar masa dukkan takardun doka, bayan ya tafi ya shawarci waɗanda abin ya shafa anan take suka ƙi aminta.
Hajiya Balkisu da ɗiyanta suka ƙi yarda su fita waje, suka rufe kan su a gidan suka yi wa jami’an kotu barazana.
Ganin haɗarin da ke cikin lamarin jami’an suka nemi agaji in da suka samu ɗaukin jami’an ‘yan sanda mata da kuma na Sibil difens don su tabbatar da zartar da hukuncin kotu.
A yanzu an fitar da mutanen daga cikin gidan, a ƙarshe Alhaji Junaidu ya dawo da gidansa hannunsa an kammala shari’un gidan a Sokoto.
A gefen Balkisu Ibrahim Bazza ta ce tun farko mijin ‘yar ta ne ya turo mata kuɗi a asusun banki nata domin tana bashi tausayi kan mutuwar aure da ya same ta, da ta ga gidan mahaifinta da take ciki ya matse ta tare da yaranta shidda shi ne ta sayi wannan gida da take ciki.
Ta ce surukinta ba shi ne ya sayi gida ba kuma takardun gida yana hannunta.
“Shekararta 14 a cikin gidan wanda na saye gidan a wurinsa Abdullahi Bature ne ke da gidan, amma shi surukina ya sayi wani a kusa da shi amma wallahi nawa ni na saye shi, yana son ya mallaki gida na ne domin ya saye gidan da ke gefe nawa ne tsakkiya, ya kawo masa cikas kuma ba shi maganar na sayar masa wai shi gidan nasa ne kuma wallahi ba nasa ba ne, ni na saye shi,” a cewarta.
Ta ce ita maganar ta na gaban kotu domin kotun kula da bayar da hayar gidaje ba ta da hurumin sauraron shari’a ta domin ni ba haya nake yi ba.
