Wutar gobara da ta tashi a safiyar Lahadi a sanadin wutar lantarki ta laƙume shaguna 50 a tsohuwar Kasuwar Sakkwato.
Wutar ta kama a layi mafi tsada a kasuwar in da ake sayar da kayan tireda da harkar canjin kuɗi da turare da sauran kayan abinci na kwali, wutar ta cinye kayan miliyoyin naira wanda har yanzu ba a ƙididdige yawansu ba.
Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa na jihar Sakkwato Alhaji Cika Sarkin Gishiri ya ce wutar ta soma ne da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Lahadi ta laƙume shaguna 50 tare da cinye kaya da yawansu zai kai miliyan 100, sai dai ba a samu hasarar rayuwa ba.
Alhaji Sarkin Gishiri ya roƙi gwamnatin jiha ta tallafawa waɗanda abin ya shafa domin su cigaba da kasuwancinsu.Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya jajanta wa ‘yan kasuwar da suka samu ibtila’in gobarar ya yi alƙawarin gwamnati za ta tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamna ya bayyana lamarin abu ne da ya zo daga Allah ya yi kira ga waɗanda shagunansu suka ƙone su barwa Allah.”Wannan gobarar ta shafi gwamnati da dukkan al’ummar jiha, ba ta tsaya kawai ga ‘yan kasuwa ba,” a cewar Gwamnan.
Ya fahimci kasuwar tana cikin manyan wuraren da ake samar da kayan more rayuwa ga mutanen jiha.
Gwamnan ya ba da tabbaci ga shugabannin ‘yan kasuwa gwamnatinsa na da ƙudirin tallafawa ‘yan kasuwa da gobarar ta shafa.Ya roƙi Allah ya kare aukuwar haka a gaba ya kuma kira da ‘yan tireda su cigaba da yin addu’a kan kasuwanci.
Gwamnan ya jinjinawa ma’aikatan kashe gobara na jiha da ‘yan kasuwa kan ɗaukin da suka kawo aka kashe wutar ba ta tsallaka zuwa wasu shaguna ba.
Tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya yi jaje ga ‘yan kasuwar ya roƙi Allah ya kare faruwar haka a gaba.
Ya yi kira ga masu shagunan su ɗauki wannan ya zo ne daga Allah.






