SERAP ta bai wa gwamnoni wa'adi su mayar wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu

SERAP ta bai wa gwamnoni wa'adi su mayar wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu

Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta yi na bai wa ƙanann hukumomin ƙasar cin gashin kai wajen kashe kudi, ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta nemi gwamnonin jihohi 36 da ministan babban birnin tarayya Abuja, da su yi lissafi tare da mayar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin ƙasar da suka karɓa a baya, ko ta gurfanar da su a gaban kotu.

Kotun ƙolin ƙasar ta ce ci gaba da riƙewa tare da kashe kuɗaɗen ƙanann hukumomin da gwamnonin jihohi 36 da ministan babban birnin kasar ke yi haramun ne.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawale Oluwadare ya fitar, kungiyar ta yaba wa kotun ƙolin kasar kan hukucin da ta yi, da ta ce zai kawo ƙarshen kashe maƙudan kuɗaɗen da ake bai wa ƙanann hukumomin don yi wa jam’a aiki ba bisa ƙa’ida ba.

“Wannan hukucin da kotun ƙolin Najeriya ta yi, ya nuna cewa akwai hukuci, ko dokar da za a iya ammfani da su wajen tuhumar gwamnonin jihohi wajen ganin sun bayar da bayanai kan yadda suka kashe kuɗaɗen ƙanann hukumomin da suka karɓa'' a cewar sanarwar.