Saudiya Ta Fitar Da Jerin Wadanda Ta Aminta Za Su Yi Aikin Hajjin Bana

Saudiya Ta Fitar Da Jerin Wadanda Ta Aminta Za Su Yi Aikin Hajjin Bana

 

Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta fitar da rukunin waɗanda  ba za su yi aikin Hajjin 2022 ba.

 

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar a jiya, waɗanda su ke da bizar da a ka saba yi idan za a shiga ƙasar, ko kuma mazauna ƙasar da su ke da shaidar iznin zama me kaɗai ne za su yi aikin Hajji.

 

Hukumar ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da shirye-shirye da tsare-tsare na aikin Hajjin bana ta sahihan kafafen ta na sadarwa.
 
A tuna cewa a bara, mahajjata 60,000, kuma mazauna Saudiya ne su ka yi aikin Hajji, kuma sai da a ka yi wa kowa allurar rigakafin korona karo biyu-biyu.
A wannan shekarar duk da an bude yawan masu zuwa aikin hajjin sai dai har yanzu ba a fitar da yawan nambar da za su hallara ba.
Alamu ya nuna za a samu sauyin ka'idojin kan aikin hajjin ganin yanda lamarin cutar Korona ke ja baya a duniya gaba daya.