Sarkuna 60 Ne Za Su Halarci Taron Makon Danfodiyo Na Wannan Shekara---Sadaukin Sokoto

Sarkuna 60 Ne Za Su Halarci Taron Makon Danfodiyo Na Wannan Shekara---Sadaukin Sokoto

Ana kyautata zaton sarakuna 60 za su halarci taron makon Shaikh Usman Danfodiyo karo na 10 da za a gudanar a wannan shekara a jihar Sakkwato.
Shugaban kwamitin tsare-tsaren taron Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ya sanar da haka a ranar Litinin lokacin da suke shirin karbar babban Malamin addinin musulunci na duniya Shaikh Zakir Naik Wanda yana cikin masu gabatar da kasida a taron, haka ma dansa Fariq Naik zai yi kasida a jami'ar Usman Danfodiyo ranar Laraba da marece.
Sadaukin Sakkwato ya ce bayan sarakuna akwai manyan malamai a ciki da wajen Nijeriya da za su halarci taron makon Shaikh Usman Danfodiyo in da makasudin haduwar don sanar da juna aiyukkan Mujaddadi in da matasa masu tasowa za su ilmanta da aiyukkan Shehu Usman Danfodiyo ya gudanar.
Taron Wanda aka soma a 27 ga Okotoba za a kare 1 ga Nuwamba, bayan kammala kasidu da wa'azin malamai daban-daban da auna fahimta a tsakanin dalibban makarantun Sikandare na jihar Sakkwato.