Sarkin Waƙa Ya Baiwa Ladin Cima Kyautar Miliyan 2, Fati Slow Miliyan 1

Sarkin Waƙa Ya Baiwa Ladin Cima Kyautar Miliyan 2, Fati Slow Miliyan 1
Naziru Ahmed Sarkin Waƙa ya gwangwaje Ladin Cima, wacce a ka fi sani da Tambaya, da kyautar Naira miliyan 2 domin ta fara kasuwanci da magance wasu matsalolinta.
Naziru Sarkin Waka ya bayyana hakan ne a Sahihin Shafinsa na Facebook.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne dai Tambaya, da ta daɗe ta na harkar fim a masana'antar Kannywood, ta tada ƙura, bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa, inda ta ce ba a ba ta sama da Naira dubu 2 ko 3 idan ta yi fim.
Wannan hira ta haifar da cecekuce tsakanin 'yan Kannywood ɗin, inda Sarkin Waƙa ya fito ya goyi bayanta.
Sai kuma ga shi a yau ya wallafa cewa ya bata kyautar Naira miliyan biyu domin ta samu ta yi wata sana'ar da za ta riƙe kan ta, kyautar an yi ta ne shi da 'yan uwansa kuma za su ci gaba da ɗaukar nauyin Ladi har zuwa abin da hali ya yi.
Nazir ya kuma baiwa Fati Slow kyautar miliyan ɗaya ta ja jari don ta gudanar da sana'a, ya bayyana hakan ne bayan ta fitar da hoton  bidiyo tana zargin Sarkin waƙa da yin lalata da wasu mata a masana'anyar Kannywood.
Nazir ya nuna ba zai kula kan kalamanta ba ya kuma yi mata alheri domin komai ya wuce.