Sarkin Musulmi@15:Tunatarwa Kan Gina Jami’ar Mata Zalla
Mai martaba ya kara cewa Jami’ar za ta mayar da hankali wurin koyar da mata musulmi sha’anin kiyon lafiya domin a wannan kasar musulmi mata na fuskatar kalu-bale in suka tafi asibitoci kan wata matsala da ta shafe su, sai ka ga maza ne za su kula da su wannan ya kara yi mana azama muka ga lalle ba makawa sai mun gina wannan jami’ar don taimakawa ‘ya’ya mata na kasar nan baki daya. Hakama ya kara da cewar Majalisarsa za ta ci gaba da taimakawa duk wani shiri na mata wanda zai kawo cigaba, domin sun san mata a kasar nan suna da kaifin basira musamman na yankin arewa, Malama Sadiya ta nuna mata na karatu da karantarwa a wannan yankin domin rubuta wadannnan littafai guda uku suna kara nuna mana yanda ilmin mata ya samu gindin zama a cikinmu. ‘Karantar da mata kamar karantar kasa ce gaba daya nan gaba kadan zamu fitowa al’umma yanda tsarin jami’ar mata zai kasance a yanzu dai wasu mutane ne masu amana da dattako muka baiwa aikin kuma ana samun gagarumar nasara. cewar mai alfarma sarkin musulmi.
Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce shirye-shirye sun kamala na gina jami’ar mata zalla kawai, ‘ban son na furta wannan maganar ba a yanzu sai karshen wannan shekarar da zamu fito da yadda tsarin zai kasance na gina Jami’ar amma ba komai tun da dalilin yin hakan ya kama’.
Sarkin musulmin ya furta haka ne a Assabar da ta gabata wurin bukin kaddamar da littafai uku da Dakta Sadiya Umar ta rubuta wadda take direkta ce a cibiyar Nazarin Hausa a Jami’ar Usman Dan Fodiyo dake Sakkwato, inda aka yi bukin a dakin taro na makarantar fasaha da kere-kere na jiha.
Mai martaba ya kara cewa Jami’ar za ta mayar da hankali wurin koyar da mata musulmi sha’anin kiyon lafiya domin a wannan kasar musulmi mata na fuskatar kalu-bale in suka tafi asibitoci kan wata matsala da ta shafe su, sai ka ga maza ne za su kula da su wannan ya kara yi mana azama muka ga lalle ba makawa sai mun gina wannan jami’ar don taimakawa ‘ya’ya mata na kasar nan baki daya.
Hakama ya kara da cewar Majalisarsa za ta ci gaba da taimakawa duk wani shiri na mata wanda zai kawo cigaba, domin sun san mata a kasar nan suna da kaifin basira musamman na yankin arewa, Malama Sadiya ta nuna mata na karatu da karantarwa a wannan yankin domin rubuta wadannnan littafai guda uku suna kara nuna mana yanda ilmin mata ya samu gindin zama a cikinmu. ‘Karantar da mata kamar karantar kasa ce gaba daya nan gaba kadan zamu fitowa al’umma yanda tsarin jami’ar mata zai kasance a yanzu dai wasu mutane ne masu amana da dattako muka baiwa aikin kuma ana samun gagarumar nasara. cewar mai alfarma sarkin musulmi.
A Wannan lokacin ne a satin da za a shiga Sarkin musulmi zai cika shekara 15 a saman wannan shugabanci kan muke tunatarwa ga Mai alfarma kan wannan aikin alheri da ya kudurta zai yi, kusan shekarru shidda da suka gabata domin akwai tsananin bukatar wannan aikin a wannan jiha ta Sakkwato da Nijeriya baki daya.
Mata da iyayensu na son karatun kimiyya kwaran gaske kan gibin da ake da shi a haujin, amma rashin samun yanayi mai kyau da inganci da yake da tabbas sai ka ga ana ja baya, amma in wannan kudirin ya cika a lokaci kaddan ana iya cike wannan gibin da ake da shi.
managarciya