Mai Alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi sanarwar a fara duba jinjirin watan Sha’aban na Shekarar 1447 daga gobe Litinin 29 ga watan Rajab wanda ya yi daidai da 19 ga watan Junairun 2026. A takardar da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a masarautar Sarkin musulmi Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar ga manema labarai ya yikira ga al’ummar musulmin Nijeriya su fara duban jinjirin watan, duk wanda ya gani ya sanar da majalisar Sarkin musulmi domin sanar da al’umma.
Ya roki Allah ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi.Watan Sha’aban yana matukar muhimmanci ga jama’ar musulmi ganin daga shi sai watan ibada waton Ramadan





