Home Rahoto Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Ramadan

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Ramadan

11
0

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Ramadan 

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ba da umarnin fara duban watan Ramadan daga gobe Talata 29 ga Sha’aban daidai da 17 ga watan Fabarairu 2026.Sarkin Musulmi ya buƙaci jama’ar muslmi su soma duban watan ne saboda watan Sha’aban ya zo ƙarshe.Shugaban kwamitin harkokin addini a majalisar kuma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ne ya fitar da sanarwar da aka rabawa manema labarai in da ake umartar musulman Nijeriya su fara duban watan kuma duk wanda ya gani ya sanar da Majalisar sarkin musulmi ko ya kira nambobin waya: 0803 715 7100, 0806 630 3077, 0803 596 5322, 0803 594 5903, 0706 714 6900.Watan Ramadan shi ne wata na tara a tsarin ƙirga na watannin Musulunci, yana da alfarma da tarin rahama da Allah ya ke saukarwa kan bayinsa.Wata ne da musulmai ke duƙufa wajen aiwatar da aiyukka ibada da tausayi ga junansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here