Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Rabi'ul Auwal

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Rabi'ul Auwal

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Rabi'ul Auwal 1447 daga gobe Assabar 29 ga watan Safar 1447  wanda ya yi daidai da 23 ga watan Agusta 2025.
Sarkin Musulmi ya ba da Umurnin ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin baiwa majalisar sarkin musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu aka baiwa manema labarai.
Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanarwa hakimi ko uban kasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.
Ya roki Allah ya kawowa Nijeriya zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Watan Rabi'ul Auwal yana cikin watanni da Musulmai ke baiwa muhimmanci a cikin watan ne aka haifi manzon Allah, da yawan mutane suna tarukka da bukukuwa don tunawa da ranar haihuwar ta Sa.
Rabi'ul Auwal ana kiransa watan mauludi a Arewacin Najeriya ganin yadda da farkon sa har karshe ba wata rana da wasu ba su wani da ya shafi tunawa da haihuwar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare Shi.