Managarciya

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin duba watan Muharram


Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya nemi al’ummar musulmi da su fara duba watan Muharam watan farko a tsarin kirgen wattanin musulunci 12 na shekara.
A wata sanarwar da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addinin musulunci na majalisar kuma wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar ya ce Sarkin Musulmi ya ba da umarnin a fara duba watan Muharam 1448 daga gobe Litinin 15 ga watan Yuni(June) 2026 daidai da 29 ga Zulhijja 1447.
Ya ba da umarnin duk wanda ya ga watan ya sanar da hakimi ko uban ƙasa na kusa da shi don sanar da Majalisar sarkin musulmi.
Watan Muharram yana da muhimmanci a tsakanin al’ummar musulmi domin akwai ibada da ladubba da ake buƙatar a yi a 9 da 10 ga watan musamman azumi.Bahaushe yana da al’adun da yake dabbakawa a 10 ga watan Muharram da yake kira watan Shara, in da wasan zumunci ke gudana a tsakanin ‘yan uwa, yara sukan yi wasan gasa Kaji da Tantabara da wasu al’adu da Malaman Musulunci ke kallon ba su tushe a addinin musulunci.

Exit mobile version