Sarkin Musulmi ya ayyana Talata daya ga  watan Rabi'ul Sani

Sarkin Musulmi ya ayyana Talata daya ga  watan Rabi'ul Sani

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya ayyana Talata ta zama  daya ga watan Rabi'ul Sani 1447  abin da ya kawo karshen watan Rabi'ul Auwal 1447  wanda ya yi daidai da 23 ga watan Satumba 2025.
Sarkin Musulmi ya aminta ne da ganin sabon watan, a wata  takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin baiwa majalisar sarkin musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu aka baiwa manema labarai.
Sarkin Musulmi bai bayyana wuraren da aka samu ganin watan ba, saboda ya gamsu da sahihan bayanan da aka samu ne ya sanar da ganin watan a hukumance.
Ya roki Allah ya kawowa Nijeriya zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Watan Rabi'ul Auwal shi ne watan Mauludi hakan ke nuna an kawo karshen bukukuwan Mauludi na wannan shekara tun da watan ya fita sabo ya shigo.