Sarkin Musulmi ya aiyana Assabar ɗaya ga watan Safar 

Sarkin Musulmi ya aiyana Assabar ɗaya ga watan Safar 
Shugaban koli na harkokin addinin Musulunci Alhaji Sa'ad Abubakar ya aiyana ranar Assabar ce daya ga watan Safar 1447 daidai da 26 ga watan Juli 2025.
A bayanin da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a majalisar sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar ya ce kwamitin ganin wata na kasa dana jihohi ba su samu wani bayani kan kan ganin wata a ko'ina cikin kasa ba.
Ya kara da cewar rashin ganin watan a ranar Alhamis 24 ga watan Juli daidai da 29 ga Muharram ya nuna watan zai kammala kwana 30 kenan, kamar yadda addinin musulunci ya shardanta.
Ya ce Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su cigaba da addu'a samun zaman lafiya a kasar baki daya.