Sarkin Musulmi a Shirye Yake, Zai Karɓi Kowacce Dokar Gwamnatin Sokoto Kafa

Sarkin Musulmi a Shirye Yake, Zai Karɓi Kowacce Dokar Gwamnatin Sokoto Kafa

 

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana shirinsa da burinsa na karɓar kowacce doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya. 

Jagoran Musulmin Najeriya, ya bayyana hakan a ranar Talata a ƙaramin zauren majalisar jihar Sokoto yayin jin ta bakin jama'a kan gyaran dokar kananan hukumomin jihar. 
Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, mamba a majalisar masarautar Sokoto kuma yana  daga cikin masu naɗin sarki ya wakilci sarkin musulmi, ya bayyana hakan.
Idan dokar ta tsallake, za a janyewa Sarkin Musulmin duk wani ƙarfin ikonsa na naɗi ko tuɓe kowanne basaraken gargagjiya a jihar. 
Haka ma an ruwaito Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Nasiru Mohammed Binji ya yi bayani kan matsayin nadin sarauta a dokance. 
Barista Nasiru ya ce ikon naɗa hakimai da sauran sarautu yana wurin gwamnati bisa la'akari da sashi na 76, ƙaramin sashi na 2 cikin baka  na kundin tsarin mulkin Najeriya. 
Fadar Sarkin musulmi  ta ce babu wata ɓaraka tsakaninta da gwamnatin jihar Sokoto ba kamar yadda ake yadawa ba. 
Fadar ta sanar da cewa, ita mai biyayya ce duk wata doka da gwamnatin jihar zata saka, ba tare da ta bijire ba, yayin da take magana kan batun janye karfin ikon sarkin Musulmi.