Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ingantaccen shugabanci nagari bai da alaka kuma bai shafi jam’iyyun siyasa ba, Daily Trust ta ruwaito.
Wike ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da titin Ogbunuabali-Eastern Bypass wadda wani jigon jam’iyyar APC Sanata Aliyu Wamakko ya halarta a jiharsa a ranar Talata.
Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su yi tunanin cewa shugabanci aiki ne na jam’iyyun siyasa, yana mai cewa aiki ya shafi tunani ne na mutum.
Wike ya bayyana cewa kauna, sha'awar sa da jajircewarsa na yi wa mutanen Ribashidima mai inganci sun bambanta shi da sauran 'yan siyasa, inji Vanguard. Shi ya sa, in ji shi, akwai ci gaba da himma wajen kara kima ga rayuwa, tasiri ga sauyi tare da karfin hali na samar da ababen more rayuwa da inganta jihar a ransa.
Wike ya ce yayin da wasu suka yi amfani da matsalar tattalin arziki a matsayin uzuri don kin yiwa jama’arsu hidima, ya sami wata hanya mai kyau don yiwa 'yan Ribas ayyuka ma su ma'ana.
Da yake kaddamar da titin Ogbunuabali –Eastern Bypass, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce Wike ya nuna cewa yana da kishin yiwa al’ummar Ribas hidima.
Sanata Wamakko ya ce ya kamata duk wata gwamnati mai ma’ana ta yi aiki don biyan bukatu da buri na al'umma.
Ya lura cewa a matsayinsa na gwamna, Wike ya yi wa jama’arsa kyakkyawan aiki