Sanata Lamiɗo Zai Tura Talakkawa da Marayu Karatu a Jami'ar Indiya da Madina
shirin kai mata jami'ar Madina don muna son mata su samu tarbiyar addini da boko a tare, ina da bukatar matan su samu dukkan karatun, shiyassa zan kai su Madina

Ɗan Majalisar dattijai mai wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ɗauki nauyin karatun jami'a na wasu ɗimbin matasa marayu da marasa galihu da ake hasashen zasu kai 100 don karanta likitanci da injiniyanci a kasar Indiya da garin Madina a kasar Saudiyya.
Sanata Lamiɗo a hirarsa da da manema labarai a Sakkwato ya bayyana cewa domin ya bunkasa ilmin yankin Gabascin Sakkwato ne ya sa ya fito da tsarin daukar marayu da marasa galihu a cikin al'umma.
"Zan tura matasa a kasar Indiya wasu su yi karatun Likitanci, wasu kuma su yi Injiniyanci sai dai ban faɗi yawan yara ba har sai naga abin da jami'ar ta tantance na yawan yara, sannan ne za mu san yawan gurabun da za ta ba mu, rukuni na farko zai tafi a watan 9, na biyu zai tafi watan 12, bayan wata uku za mu tafi mu duba kwazon wadanda muka tura in mun samu gamsuwa anan ne za mu sake tura wasu, daga hakan ne yawan adadin da muka tura zai fito ƙarara.
"Ɗalibban da za mu tura dukkan su daga yankin Sakkwato ta Gabas ne da nake waƙilta kuma duk wanda yake iya ɗaukar karatun dansa a makarantar sakandare baya cikin wannan tsarin, ɗiyan talakkawa da marayu ne zan tura gaskiya", a cewar Sanata Lamiɗo.
Kan maganar cike fom Lamiɗo ya ce "an mayar da cike fom ne a yanar gizo domin korafin da ya yi yawa, na rasa samun fom ya kai ga wadanda aka yi saboda su, bayan kammala cikewa zuwa wani sati jami'ar za ta tantance ɗalibban. Na yi haka ne domin duk yaron da ya tafi karatun, da ya dawo zai raya gidansu, haka marayu cikin ikon Allah, da farkon karatun har karshe za mu ci gaba da bibiya don tabbatar da yaran sun yi nasara."
Ba yara mata a harkar karatun ne? ya ce "ban so na yi magana ba a yanzu amma ina da shirin kai mata jami'ar Madina don muna son mata su samu tarbiyar addini da boko a tare, ina da bukatar matan su samu dukkan karatun, shiyassa zan kai su Madina, da mun kai matsaya da jami'ar za mu fitar da fom na mata, in ka duba a gefen ilmi an baro mu baya, akwai garin da ko makarantar Allo ba su zuwa a yanzu balle ta Furamari, idan a yanzu ba mu jawo wadannan ba, don su kuma su jawo na baya ka ga abubuwa za su ja baya da yawa hakan ya sa muka tsara wannan ga mutanen Sakkwato ta Gabas."
Sanata Lamiɗo ya yi kira ga ɗalibban in dan suka je wurin karatun su tsaya su yi abin da aka tura su yi, su sani kudi aka kashe masu kuma sun ga yanda kudin kasashen waje ke tashi kullum su dubi wahalar da nake yi kansu, su tsaya don su yi karatun don taimakawa al'umma, idan aka yi maka yakamata kaima ka yiwa wani.