Sanata Lamiɗo ya tallafawa mata masu juna biyu 1400 a Sakkwato 

Sanata Lamiɗo ya tallafawa mata masu juna biyu 1400 a Sakkwato 
A ranar Lahadi data gabata Sanata Ibrahim lamido ya tallafawa mata masu juna biyu  1400 da kuma samar da kulawar Lafiya kafin haihuwa a cikin kananan hukumomi takwas  dake yankinsa a Sokoto ta gabas.
Haka kuma ya ba  da kayan abinci ga  Mata zawarawa 300 mabukata don samun saukin rayuwa.
Shugabar kungiyar 'Association of concerned citizens of likes minds on youth Development' Hajiya Madina Ali Garba ce ta raba kayan a madadin Sanata Lamiɗo, ta ya bawa kokarin Sanata kan kawo gudunmuwa mafi muhimmanci ga mata a yankin ganin yadda suke da bukata ga kayan haihuwa.
Hajiya Madina ta ce Sanata yana wakiltar yankinsa ne da gaskiya hakan ya sanya ba wani gefen rayuwa da bai yi wani abun a zo a gani ba, kan haka akawai bukatar kara ba shi goyon baya domin cigaba da samar da wakilci na gari.
Babban Sakataren kungiyar Ibrahim Riskuwa ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayan yanda ya dace.
"An ba ku tallafin ne kar ku sayar, kar ku kyautar, ku yi amfani da shi domin kuna da bukata da su, a matsayin ku na masu juna biyu kuna bukatar irin wannan tallafin domin kula da lafiyar ku da abin da ke cikin naku," a cewar Riskuwa.
Ya ce sun baiwa matan abincin gina jiki da kayan tarar haihuwa don kare lafiyar jinjirin haihuwa.
Balkisu Rabah ta samu tallafin kayan haihuwa ta ce "an tallafamin da kayan haihuwa da mata ke bukata da suka hada atamfa da kayan jinjiri da sauran kayan tarbar haihuwa na mata.
Ummmu Goronyo ta ce sai godiya abin da aka yi mana domin tallafi ne da muke so da ba a bamu wannan kayan ba dole ne mazajenmu su sayo amma yanzu an samu sauki.