Sanannen Dan Kasuwar Kebbi BLB ya rasu da shekara 54
Sanannen dan Kasuwar nan dan jihar Kebbi Alhaji Balanbala Jega Dallatun Jega wanda arewacin Nijeriya ta sani da BLB ya rasu a ranar Lahadin data gaabata yana da shekara 54.
Margayi Alhaji Balanbala ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya in da ya bar 'ya'ya 21 da mata hudu.
Margayin shi ne shugaban rukunin manyan shaguna(BLB super Market) a garin Jega da Birnin Kebbi.
Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris Kauran Gandu ya ziyarci garin Jega in da ya yi ta'aziyar rasuwar margayin a ranar Litinin data gabata ya bayyana rashin sanannen dan kasuwar ba karamin rashi ba ne ga jiha baki daya.
Sarkin Kabin Jega Alhaji Arzika Muhammad Bawa ne ya karbi tawagar Gwamna amadadin iyalan margayin a lokacin gabatar da ta'aziya.
Sheikh Abbas Jega ya mika ta'aziyyar sa zuwa ga iyalai da 'yan uwa da almajirai da dukkan jama'ah bisa ga rasuwar daya daga cikin na hannun daman sa, Alhaji Bala BLB Jega.
"Alhaji Bala mutum ne, dattijo na hakika, mutum mai hakuri da sanyin hali".
"Muna rokon Allah Ya sanya Aljannar Firdaus makoma gare shi da sauran magabatanmu gaba daya."
Honarabul Mansur Musa Jega shi ma ya mika ta'aziyarsa ya ce "ina mika sakon ta'aziyyar wannan babban rashi ga iyalan mamacin, yan uwa da kuma al'ummar karamar hukumar mulki ta Jega.
"Cikin alhini nake jajantama al'ummar kasar Jega na rasuwar Alhaji Balan Bala Jega, Shugaban Rukunin BLB Super Market. Rasuwar Alhaji Balan Bala rashi ne Babba ga jama'ar garin Jega dama Jahar Kebbi baki daya."
managarciya