Sama da faɗi da kuɗin goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya sa ƙafar wando da jami'an Gwamnatinsa

Sama da faɗi da kuɗin goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya sa ƙafar wando da jami'an Gwamnatinsa


 
Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya gargadi jagororin hukumar malamai na ƙananan hukumomi da suka yi sama da faɗi da kuɗin goron Sallah dubu 30 da aka baiwa malamai, su dawo da kuɗin ko su haɗu da ɓacin ransa.
Gwamna ya yi gargadin ne a Jumu'a lokacin da yake magana da magoya bayansa a gidan Gwamnatin jiha a Sakkwato.
Ya nuna ɓacin ransa kan halayyar wasu jami'an kuɗi a ƙananan hukumomi da suka hana wa ma'aikata dubu 30 da gwamantin jiha ta amince a ba su.
"Duk wanda ya san ya rike kudin nan ya mayar da su nan take, ko a dauki mataki mai tsauri kansa."
"Duk mai tunanin zai saci kudin gwamnati ya ci banza ya sauya tunani," a cewarsa.