Gabanin babban zaben shekarar 2023 da yake kan kwana, matsalar tsaro na kara kamari a wasu jihohi, wanda hakan kan iya kawo cikas din zaben.
Yanayin rashin tsaron da ake fama da shi a Nigeria sun hada da na 'yan awaren Biafra a yankin kudu maso gabashin kasar nan, da rikicin 'yan Boko Haram da 'yan garkuwa da mutane a yankin gabashi da kuma ymmacin Arewar kasar.
Wasu kanannan rikicin da ake ganin suma za su iya rura wutar sun hada rikicin manoma da makiyaya, rikicin kabilanci a tsakiyar Nigeria wato Arewa ta tsakiya.
Masana harkokin siyasa sun fitar da wasu yankuna da jihohi da suke tunanin za'a samu tashin-tsahina a lokacin zabe.
Akwai kura babba musamman ma a jihohin da 'yan awaren Biafra suke da tasiri ko karfi wanda suka hada Enugu, Abia, Imo, da kuma Anambra, su ne a gaba-gaba da ake ganin za'a iya samun babbar matsala.
Lagos, cinkus dakin tsumma kirarin da ake mata kenan, ana ganin ita ma za'a iya samun tashin tashina a cikinta, saboda yadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya fito daga jihar kuma da yadda dan takarar jam'iyyar LP ke zaune a jihar.
Ana ganin yadda magoya bayan Tinubu da Obin kan nunawa juna yatsa, da gatsine dangane da kare muradinsu, musamman ma a yankunan da ake ganin Inyamurai sun mamaye wajen.
Jihohin Arewa maso yamma na fama da rikicin masu garkuwa da mutane musamman ma a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara.
Da yawa daga cikin kauyukan wannan jihihohin sun zama kango, sakamakon yadda aiyukan 'yan tada kayar bayan suka tashesu.
Kano Ana ganin jihar Kano a matsayin Giwa saboda yadda ake mata kallon madubi ga siyasar Nigeria ko arewacin kasar nan. Kuma jihar tana karkashin jam'iyyar APC ga kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a jihar. Hakan na barazana ga zaben, musamman ma yadda aka jiyo shugaban jam'iyya mai muki a jihar ke magana kan batun zabe.
Benue, Filato da Taraba: Wadannan jihohin sunyi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da kuma addinai da ake tunanin kuma hakan kan iya shafar zaman lafiyar jihohin a lokacin zabe.
Borno Aiyukan kungiyar ta'addancin ta Boko Haram ya ragu a yankin, to amma yadda aka ga an kaiwa dan takarar jam'iyyar PDP hari wani batu ne da ace an duba shi. Ana ganin za'a yi taho mu gama da magoya bayan jam'iyyar PDP da APC, duba da yadda jihar jam'iyyar PDP bata taba ci ba tun bayan dawowa daga dimukuradiyya.