Sakataren Gwamnatin Sakkwato ya rasa ‘yarsa da jikokinsa 3 a Gobara a Sakkwato
Sakataren Gwamnatin jihar Sakkwato Bello Muhammad Sifawa ya rasa ‘yarsa Rabi'atu Bello da jikokinsa uku sanadiyar wutar gobara da ta tashi a daren ranar Lahadi a gidanta na aure dake garin Sifawa cikin karamar hukumar Bodinga a Sakkwato.
Margayiyar tare da 'ya'yanta namiji daya da mata biyu da 'yar aikinta sun kone ne a sanadiyar wutar da ta kama gidan in da suka rasu a cikin wutar.
Mijinta waton uban yaran Muhammad Bello Yusuf babban sakatare a ma'aikatar matasa ta jiha yana raye da diyanta biyu maza sun kubuta daga cikin iyalan.
Margayiyar ita ce babbar 'yar Sakataren Gwamnati ta yi shahada wurin kokarin kubutar da 'ya'yanta a cikinn gobara.
managarciya