Sakataren Gwamnatin Sakkwato Ya Bayyana Tsayawarsa Takarar Gwamna

Sakataren Gwamnatin Sakkwato Ya Bayyana Tsayawarsa Takarar Gwamna

Sakataren Gwamnatin Sokoto Malam Saidu Umar Malam Ubandoma ya fito takarar Gwamna a zaben 2023.
Hadiman Sakataren Gwamnatin Abubakar Muhammad Jibo da Nafi’u Muhammad Lema  ne suka tabbatar da takarar ga Managarciya a birnin Sakkwato.

Sun bayyana cewa Malam Ubandoma ya ɗauki wannan matsayar bayan tuntuɓa da matsin lamba da ya samu daga wasu masu kishin jahar Sokoto.
Sakataren gwamnati shi ne mutum na uku a jam'iyar PDP da ya bayyana takararsa ta gwamna a zaɓe na tafe.

Bayan Sagir Bafarawa da Mukhtari Shagari sai wannnan a yanzu su ne suka bayyana tsayawar domin su gaji gwamna mai ci waton Aminu Waziri Tambuwal.