Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita  hayyacinsu a Kano

Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita  hayyacinsu a Kano

 

Daga Ibrahim Hamisu

 

Rahotonni daga yankin rukunnin masana’antu na 3 da ke Sharada a jihar Kano na cewa, wasu mazauna unguwar Mundaɗu da dama sun fita daga hayyacinsu sakamakon shaƙar hayaƙin wani sinadari.

 
Da yammacin jiya Juma’a ne dai gidan radiyon Freedom ya fara  bada Labarin faruwar lamarin, yana mai cewa iftila’in ya faru ne sakamakon fashewar wata tukunyar sinadari ta masana’antu wadda ke ɗauke da guba.
 
Kazalika Rahotan ya  nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wani wurin masu yin sana’ar gwangwan da ke unguwar inda mai unguwar yankin Malam Magaji Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin yana mai cewa an garzaya asibiti da mutane da dama.