Sakacin Gwamnati: Jirgi ya sake nutsewa da mutane 12 a Sakkwato 

Sakacin Gwamnati: Jirgi ya sake nutsewa da mutane 12 a Sakkwato 
An sake samun damuwa a karamar hukumar Shagari in da jirgin ruwa ya nutse da mutane 12 a  karamar hukumar Shagari ta jihar Sakkwato abin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu mace da Namiji, 10 suka samu rauni.
Hatsarin ya faru ne da daren ranar Alhamis a gulbin Shagari in da mutane suka shiga cikin damuwa da kaduwa kan jirgi ya nutse da mutane da babur guda biyu da sauran kayan amfani, a wata daya jirgi uku ya nutse a ruwa a Sakkwato.
Nasir Umar wanda lamarin ya faru gaban idonsa ya ce "jirgin ne ya nutse da mutane 12 da ya dauko daga garin Jaranja zuwa Ruggar Buda a mazabar Lambara,  kan haryar ne ya fadi, a daren Alhamis   aka fitar da mutum biyar sun samu rauni.
"Mutanen gari da suka kawo dauki ne suka taimaka kuma su ne suka ci gaba da aikin har a Jumu'a, an yi nasarar fitar da mutum shida, biyar a raye daya ya mutu, mace guda ta bata ba a ganta ba.
"Kan zurfin ruwan har yanzu ba a samu ceto mace daya da ta rage a ruwan ba, ana dai sa ran ba ta da rayuwa a yanzu," a cewarsa.
Ya yi tir da halin da gwamnati ta nuna kan lamarin in da har aka ciro mutanen ba wani wakilin gwamnati da ke wurin, mutane ne suke taimakon junansu, a gaban sarkin ruwa.
Kabir Lumu ya nuna faduwar jirgi da ake samu a kwanan nan sakaci ne na gwamnati domin ta ki samar da hanyoyin mota a wuraren da ruwa suka mamaye kuma sun ki samar da tsari mai kyau a harkar sufurin jiragen, sun kyale talakawa suna kowa tasa ta fisshe shi, matuƙar Gwamnatin Sakkwato ba ta dawo cikin hayyacinta ba kan wannan matsalar za a cigaba da rasa mutane a jirgin ruwa.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin mai baiwa gwamnan Sakkwato shawara kan Hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha Aminu Liman Bodinga ya ce sun tura jami'an su in da lamarin ya faru don ba da taimakon da ake bukata.