Rusau a Abuja: Wani magidanci ya mutu bayan an rushe masa gida
Ƴan asalin garin Karsana da ke cikin Karamar Hukumar Birnin Abuja sun shiga jimami bayan rasuwar Luka Iliya, wanda ya rasu sa’o’i bayan an rushe masa gida a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa an rushe gidan marigayin da na wasu mazauna garin da dama, ciki har da fadar mai gari a ranar Juma’a.
Daily Trust ta rawaito cewa an ce Luka Iliya ya kamu da rashin lafiya bayan radadin ganin an rushe masa gida, inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja a Gwagwalada, amma ya rasu da safe a ranar Lahadi.
Shugaban matasan Karsana, Zakari Baba, ya bayyana cewa an kuma rushe cocin garin tare da wasu gidaje yayin da yawancin mazauna garin suka tafi gonaki da wuraren aiki.
A ranar Litinin, rikici ya ɓarke yayin da ‘yan sanda suka hana mazauna shiga garin don kwashe kayayyakinsu. An zargi jami’an tsaro da harbin mazauna biyu – Sunday Danjuma da Jacob Audu – a ƙafafu da hannuwa tare da amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa jama’a.
Shugaban karamar hukumar Christopher Zakka Maikalangu, ya ziyarci yankin tare da yin Allah-wadai da aikin rusau da bai samu izini ko sanarwa ba, yana mai barazanar ɗaukar mataki na doka kan mai masu rusau din. Ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike, da su gaggauta shiga lamarin don tallafa wa waɗanda suka rasa matsugunnai.
managarciya