Rundunar sojin ƙasa za ta ɗauki sabbin sojoji 13,000 – Oluyede
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta bayyana cewa tana shirin ɗaukar sabbin jami’ai 13,000 kafin ƙarshen shekarar 2025 domin ƙarfafa yawan ma’aikatan da ke aiki a yanzu.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana haka a Abuja yayin da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Soji, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yar’Adua, ya kai masa ziyara.
Oluyede ya ce rundunar na fuskantar matsin lamba wajen inganta aiki da walwalar jami’ai, yana mai bayyana ƙarancin kuɗaɗe da rashin isassun wuraren kwana ga sabbin sojoji da ake sa ran ɗauka.
Ya bukaci a samar da wani tanadin kuɗi na musamman a wajen tsarin kasafin kuɗi na "envelope" don tallafa wa rundunar.
Sanata Yar’Adua ya amince da buƙatar, yana mai cewa akwai buƙatar cire rundunar daga tsarin envelope budgeting domin ƙara wa rundunar kuɗin da take buƙata.
Kwamitin ya raba kansa zuwa ƙungiyoyi biyu don duba rundunonin soji a Borno, Katsina, Sokoto, Kebbi da Legas, tare da tabbatar da ingantaccen amfani da kasafin kuɗi.
managarciya