Rundunar Soja Yankin na 8 sun gargadi mutanen Sakkwato
Rundunar Sojan kasa yanki na 8 sun jawo hankalin mutanen kauyen Tankwale a karamar hukumar Illela dake jihar Sakkwato kan a atisayen harbi da za su gudanar a ranar Assabar.
A wata takarda da jami'in hulda da jama'a na rundunar Laftanar Kanal Ikechukwu Stephen Eze ya aikawa manema labarai a Sakkwato ya ce hidikwatar rundunar soja yanki na takwas dake Sakkwato za ta gudanar da atisayen harbi ga sojan da suka samu horo(BBC) 01/2023, a Tankwale ranar Assabar daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Ya ce ana yin atisayen ne domin sanin karfi da aikin makamai da sanin matakin da suke ciki a hannun sojoji, Kuma hakan zai Kara kwarewar iya harbi ga jami'an soji.
"A wurin atisayen za mu fito da sojoji da kayan aiki masu yawa, kan haka muke shawartar mutanen gari kar su firgita ganin sojoji na zirga-zirga da jin karar bindiga ana harbi, za mu tabbatar da kariyar rayuwa da dukiyoyin jama'a a lokacin atisayen.
"Muna son magidanta musamman al'ummar kauyen Tankwale makiyayansu da Manoma da sauran kauyukka makwabta, su kaucewa wurin da za a yi atisayen," a cewar bayanin.
Shugaban rundunar a yanki na 8 Mejo Janaral Godwing Mutkut ya godewa hadin kan da mutane ke bayarwa domin samar da zaman lafiya.
managarciya