Ministan Sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaechi ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Amaechi ya baiyana cewa zai tsaya takarar ne a yau Asabar a cikin turakarsa ta Facebook.
Ministan ya ce zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa domin ya gaji Muhammadu Buhari.
“ina sanar muku da aniya ta neman zama shugaban kasar Nijeriya a 2023,” in ji shi.





