Rikicin Siyasar Gombe: Gwamnonin APC Sun Ziyarci Gwamna Inuwa
Sannan sai ya yi kira ga shugabanni da cewa su sani banbanci ra’ayi a siyasa dole amma ya zama an magance shi ta hanyar lumana ba tare da an samu tashe-tashen hankali ba. Da yake maida jawabi gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, cewa yayi gwamnonin jam’iyyar APC sun zo jihar Gombe ne karkashin jagorancin gwamnan Katsinan Aminu Bello Masari, dan su jajanta musu bisa rasuwar wasu mutane da ya faru a rikcin siyasar da ya faru juma’ar da ta gabata. Yace wannan ziyara ta gwamnonin APC ta nuna kauna da suke yiwa jama’ar Gombe ne, dan haka yace suna godiya bisa kaunar da suka nuna wa al’ummar Gombe kan wannan rikici da ya faru
Rikicin cikin gida na jam’iyyar APC da ya faru a ranar juma’ar da ta gabata tsakanin gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da tsohon Uban gidan sa Sanata Muhammad Danjuma Goje, a lokacin da aka tare Sanatan daga filin jirgin sama aka hana shi shigowa gari da ya haifar da rikicin da har aka samu asarar rai da dukiyoyin al’umma.
Ganin wannan rikici na cikin gida ne na ‘Ya’yan jam’iyya daya hakan ya tada hankalin ‘ya’yan jam’iyyar a kasa baki daya inda har gwamnonin jam’iyyar suka hadu suka jajantawa al’ummar jihar Gombe kan faruwar rikcin ganin an tafka mummunan asarar rai da ta dukiya.
A wannan rana ta juma’a 19 ga watan Nuwamba gwamnonin jam’iyyar APC suka turo wakilci karkashin jagorancin gwamnan jihar Katsina Sanata Aminu Bello Masari, da gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa, zuwa Gombe suka jajantawa al’ummar Gombe ta wajen gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.
Da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin Gombe Shugaban tawagar Aminu Bello Masari, yace sun zo Gombe ne dan jajantawa Gombawa na rikicin siyasar da har wasu suka rasa ran su, inda yace ba yadda za’ayi aci gaba a kasa muddin ba zaman lafiya.
Yace a Siysasa akwai hanyoyi da yawa da ake magance banbancin ra’ayi, tun daga kan kansila da ma kowanne irin mukami kake rike da shi ya zama dole ka yiwa al’umma adalci, adalci kuma ya kan haifar da zaman lafiya kuma sai da lafiya ake neman abinci ake komai a rayuwa.
Masari, yace tarihin shugabanci shi ne dan a kare rayuka da dukiyoyin al’umma idan babu adalci ba yadda za’ayi a samu shugaba nagari
Sannan sai ya yi kira ga shugabanni da cewa su sani banbanci ra’ayi a siyasa dole amma ya zama an magance shi ta hanyar lumana ba tare da an samu tashe-tashen hankali ba.
Da yake maida jawabi gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, cewa yayi gwamnonin jam’iyyar APC sun zo jihar Gombe ne karkashin jagorancin gwamnan Katsinan Aminu Bello Masari, dan su jajanta musu bisa rasuwar wasu mutane da ya faru a rikcin siyasar da ya faru juma’ar da ta gabata.
Yace wannan ziyara ta gwamnonin APC ta nuna kauna da suke yiwa jama’ar Gombe ne, dan haka yace suna godiya bisa kaunar da suka nuna wa al’ummar Gombe kan wannan rikici da ya faru
Gwaman Inuwa Yahaya, yace duk dan Gombe ya san yana kokari wajen ganin an zauna lafiya a jihar Gombe, kuma kamar yadda gwamnan Katsina ya fada haka ne idan babu zaman lafiya ba abunda dai ci gaba.
“A kullum ina kira da a zauna lafiya domin idan babu zaman lafiya ba yadda za’ayi a samu ci gaban da ake hankoro domin mun yi alkawarin cewa za mu kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matsayin mu na gwamnati” inji shi.
managarciya