Rikicin shugabanci a PDP: Gwamnoni sun kira taron gaggawa

Rikicin shugabanci a PDP: Gwamnoni sun kira taron gaggawa
Rikicin shugabanci a PDP: Gwamnoni sun kira taron gaggawa

Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kira takwarorinsa Gwamnonin PDP a wani taron gaggawa da za a gudanar a gobe Alhamis da karfe biyar na marece.
 
Tambuwal bayan tuntubar takwarorinsa ne ya yanke shawarar kiran taron domin tattauna halin da jam'iyar PDP take ciki a yanzu.
 
A bayanin da darakta Janar na kungiyar gwamnonin Honarabul Maduabum ya ce gwamnonin sun yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da mabiya jam'iyarsu da su yi hakuri ana kuma kokarin dawo da martabar jam'iyar ta zama kan gaba a kasa baki daya.