Rikicin Shari'a: Gwamna Abba Ba Zai Maida Takardun Hukuncin Kotu ba---Lauyan NNPP

Rikicin Shari'a: Gwamna Abba Ba Zai Maida Takardun Hukuncin Kotu ba---Lauyan NNPP

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ki amincewa da bukatar kotun daukaka kara na dawo da takardun hukunci watau CTC. 

Legit ta samu labari lauyan gwamnan jihar Kano a shari’ar da aka yi, Wole Olanipekun (SAN) ya fitar da wata wasika a matsayin martani. 
A doguwar wasikar, Wole Olanipekun (SAN) ya ce kotun daukaka kara ba ta da hurumin gyara takardun hukuncin domin lokaci ya wuce. 
Lauyan yake cewa a sashe na 285 (7) na kundin tsarin mulki, abin da dokar kasa ta ba kotun daukaka kara ta yi hukunci kwanaki 60 kacal ne. 
Wadannan kwanaki sun kare daga ranar 18 ga watan Nuwamba, tun a makon jiya kenan, yanzu abin da NNPP ta ke so shi ne zuwa kotun koli. 
The Nation ta ce kwararren lauyan ya ce yanzu ya ragewa kotun koli ta yanke hukuncin da ta ga ya fi dacewa bayan tuntuben alkalamin. 
Kuskuren da aka samu ya jawo sabani da rabuwar kai tsakanin magoya baya a jihar Kano, har ta kai wasu su na cewa abin ya fi karfin kuskure. 
"A kaddara a takardar hukuncin akwai wasu kura-kurai, na tuntuben alkalami ko makamancisu, muna jawo hankalinku cewa lokaci ya kurewa kotun daukaka kara daga ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba 2023 Sai a kotun koli kurum za a duba maganar neman yin duk wani gyara. 
Sannan sashe na 285 (7) na kundin tsarin mulki ya ce kotun daukaka kara ba za ta iya daukar wani mataki a shari’a ba bayan kwanaki 60." Lauyan NNPP a shari'ar Kano, Wole Olanipekun.