Rikici ya Kunno kai tsakanin gwamnatin Sakkwato da majalisar dokoki
Rikici ya kunno tsakanin gwamnatin Sakkwato da Gwamna Ahmad Aliyu ke jagoranta da majalisar dokokin jihar in da majalisar ta yi barazanar hukunta kwamishinan Makamashi na jiha Honarabul Sanusi Danfulani matukar bai amsa gayyatar da ta yi masa ba a ranar Talata mai zuwa 5 ga watan Agusta.
Majalisar dokokin ta nemi Kwamishina ya bayyana gabanta saboda walakanta 'yan majalisa da ya yi a lokacin da suka fita rangadi a hukumance, mambobin kwamitin kimiya da fasaha sun sanar da zagayen a ma'aikatarsa, amma da suka zo kwamishina da sauran manyan ma'aikata ba kowa ba tare da sanar da kowane uzuri ba.
Shugaban kwamitin Honarabul Awaisu Aliyu ya nuna bacin ransa matuka kan abin da kwamishina ya yi, "a bayyane ƙarara wannan rashin girmamawa ne da nuna kin martaba majalisar dokoki"
Awaisu ya ce "kwamiti a hukumance ya sanar da ma'aikatar Makamashi kan ziyarar gani da ido da zai kawo amma a lokacin da muka zo kwamishina da manyan ma'ikatan wurin ba wanda yake nan, kuma ba wani uzuri a rubuce ko a baki da aka bar mana don a sanar da mu."
"Wannan kaskanta hakkin da tsarin mulki ya bamu ne, kan yin zagayen gani da ido kan aiyukkan gwamnati, mun umarci Kwamishina ya zo ranar Talata don ya yi bayani kan abin da ya yi mana, sabawa umarnin kuwa za a dauki matakin ladabatarwa kansa," ya yi gargadi.
Majalisar ba ta sanar da Irin hukuncin da za ta yi wa Danfulani ba in bai halarta ba.
Wakilinmu ya kira Honarabul Sanusi Danfulani kan ko zai karba gayyatar da majalisa ta yi masa ya ce "zan kira ka daga baya."
Majalisar dokokin ta jiha da yawan Sakkwatawa ba su ganin su da wata kima ganin yanda suka zama 'yan amshin shatar gwamnati, ba ruwansu komai gwamna ya aiwatar daidai ne.
Wani dan Sakkwato Aminu Muhammad ya ce ai 'yan majalisar dokokin jiha ba wani abu da suke yi a majalisa da ya wuce karbar albashi, amma aikin da suka je majalisa don shi ba su yi, ka barsu dai da yi wa gwamna biyayya.
"A kullum dan majalisa jira yake yi a turo sako daga wurin Gwamna su amince da shi ba tare da duba komai ba, haka suka amince da sauya tsarin dokokin masarauta da hukumar zakka da wakafi ba da son jama'a aka yi haka ba."
"Suna gani gwamna yana fara yin aiki majalisar zartarwa ba ta yi zama kan aikin ba amma ba magana, cikinsu da yawa wasu hakkinsu na majalisa suna fadin ba a ba su amma ba su magana." In ji Aminu.
Ya ce haka a shekara da ta gabata Kwamishinar lafiya ta yi masu, an san su Damisar Takarda ne komai ba su yi dole mukaraban gwamnati su rena su, amma za a jira a gani ko baraka ce ta Kunno kai tsakaninsu ko don Majalisar dokokin ta gaji da cin kashin da ake yi masu.
Ya ce in dai har martaba kansu ce suke son ta dawo abu ne mai kyau amma in sun yi haka ne don kawai sun rena Kwamishinan Makamashi Sakkwatawa ba za su yafe masu ba, musamman yanda suka bari wannan gwamnati na cin karenta ba babbaka ba tare da tsawatarwa ba.
managarciya