Rikici Ya Kunno Kai A PDP Kan Zaɓen Mataimakin Atiku

Rikici Ya Kunno Kai A PDP Kan Zaɓen Mataimakin Atiku
 
Wani sabon rikici ya kunno kai a kan zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ke ƙara tuntuɓar masu ruwa da tsaki.
Wani sabon rikici ya kunno kai a kan zaɓin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a Jam’iyyar PDP.
An ruwaito Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yana barazanar ficewa daga PDP muddin Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban kasa na 2023.
Wike ya yi barazanar ne bayan an gabatar da sunan Okowa a cikin mutanen da ake so su yi takara tare da Atiku, a lokacin taron da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi da gwamnonin jam’iyyar a kan zabin wanda zai tsaya tare da shi.
A ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da Atiku Abubakar yake yi, zai gana da tsofaffin gwamnoni da ministocin jam’iyyar a karshen makon nan a Abuja.
Ko a ranar Laraba, dan takarar ya yi irin wannan zama da gwamnonin PDP.
Wata majiya mai masaniya game da zaman da za a yi a karshen mako ta ce hakan wani bangare ne na kokarin dan takarar na “daidaita bukatun dukkan sassan jam’iyyar kafin ya kai ga zabo mataimakin nasa.”
Majiyar ta ce a taronsa da su, gwamnonin sun nemi ya zabi daya daga cikinsu, ciki har da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda ya zo na biyu a zaben fidda-gwani.