Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara Da Mayar Da Su Saniyar Ware

Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara Da Mayar Da Su Saniyar Ware

 

Rikicin da ya biyo bayan sakin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar  APC ya dauki sabon salo. 

Shugaban uwar jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya aike da wasikar kar-ta-kwana ga dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a rahoton Vanguard. 
Da alamun jam'iyyar APC na gab da shiga irin rikicin da ya karade jam'iyyar adawa ta PDP Shugaban uwar jam'iyyar APC ya tuhumci Asiwaju Bola Tinubu da kokarin mayar da su saniyar ware 
A wasikar da Adamu ya aike cikin daren jiya(Laraba), ya tuhumci Tinubu da saba alkawarin da yayi da mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar game da mukaman kwamitin yakin neman zaben.
Abdullahi Adamu ya ce alkawarin da aka yi shi ne a nada shi matsayin mataimakin shugaban kwamitin; a nada Sanata Abubakar Kyari matsayin jagoran Arewa, sannan Hon Emma Eneukwu matsayin jagoran kamfen na Kudu. 
Hakazalika a nada Sakataren APC, Iyiola Omisore matsayin mataimakin kwamitin (lamuran jam'iyya); Sakataren shirye-shirye Alhaji Sulaiman Argungu matsayin Jagoran shirye-shiryen kamfe, Hon Victor Giadom matsayin jagoran kamfe na yankin Kudu maso kudu, da sauransu.
Ga kadan daga cikin wasikar da Managarciya ta yi kicibis da ita: 
Wannan wasika ta zama wajibi dubi ga abubuwan da suka faru kwanakin nan game da nadin mukaman kwamitin yakin neman zabe inda wasu mambobi suka saki jerin sunayen ba tare da izinin uwar jamiyya ba." 
"Mun yi mamakin yadda aka saki sunayen mambobin kwamitin a ranar 23 ga Satumba 2022. 
"Wannan ya sabawa ka'idojinmu da yarjejniyar da ni da kai muka yi kan yadda za'a tsara kwamitin da shugabanninsa." 
"Idan muka bari aka samu rabuwan kai cikin jam'iyyar, hakan zai kashe kuzarin kamfen kuma zai batawa 'yan jam'iyyar rai." "Hakazalika hakan zai baiwa 'yan adawa daman cin zaben a bulus."