Rashin Tsaro:- Kungiyar fataken Shanu a Zamfara tayi na'am da dokar da gwamnati ta saka
Rashin Tsaro:- Kungiyar fataken Shanu a Zamfara tayi na'am da dokar da gwamnati ta sa.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Hadaddiyar kungiyar fataken shanu ta kasa reshen jihar zamfara ta ja kunnen ya yanta dake fadin jihar dasu kasan ce masu biyayya ga sabuwar dokar da gwamnati ta saka, ta hana saye ko sayar da Dabbobi a duk fadin kasuwannin dake jihar.
Kwamred Aminu Gusau shugaban kungiyar ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin jiha.
Yace "kungiyar mu tana daya daga cikin wayanda naji dadin wannan dokar saboda muna fuskantar barazana wajen gudanar da harkar sana'ar tamu, hasali ma ga kasuwan nin dake a kana nan hukumomi.
" Amma idan aka rufe kasuwa da hana sayar da man fetur da kuma hana hawan mashin fiye da mutun ukku aka kuma rage zirga zirgar mashuna da dare insha Allahu za'a cimma abun da ake gurin a cimma.
Kwamred ya bayya cewa su masu biyayya ne ga gwamnati a don haka ya zama wajibe gare su da su tabbatar kowane mamban su dake birni da kauye ya bi umurnin gwamnati in kuma ya ki to su zasu fara daukar mataki akan sa.
Gusau daga nan sai yayi kira yan kungiyar tasa dasu kara yin hankuri domin gwamnati ta sa wannan dokar ne saboda ceto rayukkan jama'a da kuma dukiyoyin su a hannun yan ta'addar da su kaki yarda da zaman sulhun da akayi dasu .
Idan baku manta baa satin da ya gabata ne gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Matawalle ya saka dokar rufe duk kasuwanni masu ci sati sati, da kasuwar sayar da dabbobi, da sayar da man fetur a jarka, da kuma rufe duk gidan man da baya cikin hedikwatar karamar hukumar mulki a duk fadin jihar.
A sakamakon hakan mun samu wasu rahotanin da ke cewa mutane a wasu kauyukka sun fara ganin yan ta'addan suna yawo jaye da masunan a dalilin karewar man fetur.
managarciya