Home Rahoto Rashin tsaro:.Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi huɗu

Rashin tsaro:.Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi huɗu

6
0

Rashin tsaro:.Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi huɗu

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da rufe kasuwannin shanu a wasu kananan hukumomi hudu na jihar nan take, sakamakon matsalolin tsaro.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar, inda ya ce an dauki matakin ne domin dakile ayyukan ta’addanci da ake zargin ana gudanarwa a wadannan kasuwanni.

Sanarwar ta bayyana cewa kasuwannin sun zama wuraren aikata laifuka kamar satar shanu, kisan kai, garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, karbar haraji ba bisa ka’ida ba, safarar makamai da kuma harkokin kudi ba bisa doka ba.

Haka kuma ta ce ‘yan ta’adda na kai hare-hare kan ‘yan kasuwa, suna satar dabbobi tare da kawo cikas ga hanyoyin samar da abinci, lamarin da ke haddasa asarar tattalin arziki da kuma barazana ga rayuwar al’ummomi.

Kasuwannin da abin ya shafa sun hada da guda 14 a karamar hukumar Alkaleri, ciki har da Alkaleri, Mansur, Futuk, Yalo, Gwana, Yalon Gurza, Kuka, Rimi, Pali, Bokwas, Kwaimawa, Mai Ari, Gajin Duguri da Maina Ma’aji.

A karamar hukumar Kirfi kuwa, an rufe kasuwannin Lariski Bara, Sharfuri (kasuwar dare), Cheledi da Boli.

Haka kuma a Tafawa Balewa, kasuwanni biyar ne abin ya shafa, wato Burga, Bununu, Ball, Kulumbo da Zwall.

A karamar hukumar Bauchi kuma, kasuwar shanu ta Liman Katagum ta shiga cikin jerin kasuwannin da aka rufe.

Gwamnatin jihar ta ce matakin na wucin gadi ne, kuma zai ci gaba da aiki har sai an samu gagarumin sauyi a harkokin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here