Rashin Kuɗi: Gwamnoni Sun Ba Buhari Shawarar Ya Kori Ma'aikata Ya Janye Tallafin Mai Da Kuma Tsuke Bakin Aljihu

Rashin Kuɗi: Gwamnoni Sun Ba Buhari Shawarar Ya Kori Ma'aikata Ya Janye Tallafin Mai Da Kuma Tsuke Bakin Aljihu

 
Wani rahoto na musamman da Premium Times ta fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022, yace an kawo shawarar a sallami ma’aikatan da suka kai shekara 50. 

Gwamnoni sun yi kira ga Muhammadu Buhari ya yi hakan lura da yadda ake fama da matsin lambar tattalin arziki, da nufin hakan zai magance rashin kuɗi. 
Wadanda suka halarci wannan zama sun shaidawa jaridar cewa gwamnonin sun nuna damuwa kan halin tattalin arzikin da kasar nan ya samu kan shi a yau. 

Ma’aikatan gwamnatin tarayya ba su wuce 89,000 ba, amma za su lakume N4.1tr daga kasafin kudin bana. 
Albashi da alawus na ma’aikatan zai ci kusan 25%. Hakan ta sa gwamnonin su ka bada shawarar a sallami ma’aikatan da shekarunsu sun kai 50. Ba za a iya cewa ga abin da masu shekarun nan suke karba ba.
Rahoton yace gwamnonin sun nemi a janye tallafi man fetur, ayi watsi da tsare-tsaren SIP da NPRGS, sannan a rage kwangilolin da ake ba ‘yan majalisa. 
Wata shawara daga bakin gwamonin ita ce a tabbata an gama aikin matatar Dangote, sannan a dage da hako mai da gas yayin da ake rikicin Rasha da Ukraine. Baya ga haka gwamnonin sun nemi a canza yadda ake karbar haraji, sannan a hana ma’aikatu fita kasashen wajen na tsawon shekara daya domin rage facaka.