Rashin halartar Alkali ya sa an dage shari'ar da tsohon sarkin maru ya shigar

Rashin halartar Alkali ya sa an dage shari'ar da tsohon sarkin maru ya shigar.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Rashin halartar alkali mai shari'a, Mai shari'a Bello Shinkafi a kotu, ya dakatar da ci gaba da sauraron karar da mai martaba sarkin Maru na jihar Zamfara, Abubakar Ibrahim ya shigar akan Sufeto Janar na 'yan sanda, IGP da wasu mutane biyar.
Sauran mutane biyar da ake karar sun hada da tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Bala Bello Maru, da darakta Ma'aikatar yan sandan ciki na jiha DSS, da Kwamishinan 'yan sanda da Darakta Janar na Ma'aikatar yan sandan ciki DSS.
Sarkin da aka sauke ya fara shigar da karar ne a babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, wanda daga bisani mai shari’a Fatima Aminu ta mika karar zuwa babbar Kotun Jihar Zamfara, inda ya ke kalubalantar take hakkinsa na dan adam, kama shi ba bisa ka’ida ba, tsare shi da kuma bata masa suna.
Alhaji Abubakar Maru yace yana neman naira miliyan 6.5 a matsayin diyya.
Alkalin da ke sauraron karar, Jastis Bello Shinkafi ya dage shari’ar ranar Talata da ta gabata zuwa Laraba, 11 ga watan Agusta da muke ciki saboda alkalin bai shirya ba.
Haka zalika ko a ranar ta laraba Alkalin bai samu halar tan zaman kotun ba, saboda an ce ba shi da lafiya.
A zantawar da manema labarai sukayi da lauyan mai shigar da kara Mista Sam Anosike ya ce, za a sanar da sabon ranar yanke hukunci daga baya duk wanda keda hannu a shari'ar za'a sanar dashi.
Idan baku manta ba an dakatar da Sarkin masarautar Maru, Abubakar Ibrahim, a watan Oktoban shekarar 2019, sannan kuma Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya cire shi daga mukaminsa, bisa zarginsa da hannu a cikin rashin tsaro da ke addabar jihar.
An dai tsare sarkin har na tsawon watanni 11 a gidan gwamnati, dake Gusau, babban birnin jihar Zamfara.