Home Siyasa Rashin adalci ne jam’iyyar PDP ta mara wa Tinubu baya a zaben...

Rashin adalci ne jam’iyyar PDP ta mara wa Tinubu baya a zaben 2027 – Jam’iyyar PDP tsagin Turaki

2
0

Jam’iyyar PDP bangaren Tanimu Turaki ta bayyana cewa rashin adalci da rashin da’a ne ga jam’iyyar ta goyi bayan shugaban Nijeriya Bola Tinubu a zaben 2027. Wannan na daga cikin jawabin Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Ini Ememobong, ne ya bayyana haka a gidan talabijin na Arise.

Ememobong ya ce duk wani sulhu da ake yi tsakanin bangarorin jam’iyyar dole ne ya karfafa matsayin PDP a matsayin jam’iyyar adawa, ba tare da mayar da ita karkashin APC ba.

Tsagin Turaki ya tabbatar da cewa tattaunawar sulhu da bangaren Wike an fara ne a ranar Talata kuma ana samun sakamako mai kyau, inda dukkan bangarorin ke nuna son ganin jam’iyyar ta samu hadin kai kafin taron kasa na 29–30 ga Maris, 2026.

Ya kara da cewa PDP zata yi duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar, ciki har da janye duk shari’o’in da ke gaban kotu idan an kammala tattaunawar sulhu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here