Rantsar Da Isah Sadik  Achida: Wamakko Abin Dogara Ne A Siyasa

Rantsar Da Isah Sadik  Achida: Wamakko Abin Dogara Ne A Siyasa

Muhammad Nasir.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko jagoran jam’iyar APC na kasa kuma daya daga cikin jagorori a Nijeriya da suka kafa jam'iyar APC suka yi mata dawainiya  har ta kai ga kowa naso da mararinta.

Sanata Wamakko wanda da yake siyasa domin taimakon jama’arsa da kokarin ganin talaka ya samu walwala da 'yancinsa a koyaushe.

Jam'iyarsa ta APC reshen jihar Sakkwato tun bayan kare zaben mazabu da aka yi wata bakwai da suka wuce ta fada cikin wani karamin rikicin cikin gida, wanda mutane da dama suke ganin wani abu ne na neman suna da kokarin mayarda tafiyar Wamakko baya, a haka aka cigaba  da wannan tirka-tirka har zuwa zaben shugabanni na jiha in da aka samu shugabanni har uku da aka bayyana a gaban shari'a, waton Mainasara Sani da Alhaji Sirajo da Isah Achida,  kafin haka mutanen Sakkwato Isah Sadik Achida wanda yake biyayya ga Sanata Wamakko kawai suka sani.

Wutar rigimar ta fito fili  ne a lokacin da Ministan shari'a kuma lauyan gwamnatin tarayyar Nijeriya Abubakar Malami ya fito karara ya bayyana yana tare da  bangaren mutane dake jayayya da Sanata Wamakko don ganin ya hana su rawar gaban hantsi duk da dimbin alherin da ya yi masu, amma sun aminta da lokaci ya yi da su saka masa da sharri ta hanyar lika masa abin da bai ji bai gani  ba, a tunaninsu sai ka yi wa Sanata Wamakko Sharri sannan ka ke samun galaba kansa.

Ganin hakan ya sa wasu ke ganin lokaci ya yi, ga duk wanda ya jingina da Sanata Wamakko zai  yi hawaye, ya rasa makama,  zai koma dan kallo a siyasar jiharsa ta haihuwa, kuma dolensa ya hakura da duk wani habaici da kazafi da musgunawa da za a yi masa.

Alhaji Isah Sadik Achida da sauran shugabanni 37  da aka zaba tare da shi ba su girgiza ba, sun kara rike yakinin da suke da shi cewa shugabansu jagora ne ba ya janye duk wanda ya dogara da shi, iya karfin da Allah ya yi masa zai yi amfani da shi don ya sanya magoya bayansa dariya.

Ni mai rubutu na tabbatar da hakan a lokacin da labarin rantsar da Isah Achida ya riske ni, anan ne na ce WAMAKKO ABIN DOGARA NE A SIYASA.

Da yawan wasu jagororin siyasa sukan tafi su bar magoya bayansu a lokacin da suka ga wata guguwa ta taso da nufin ta cinye su gaba daya, sabanin Wamakko da ba zai razana ba, kuma zai shiga gaba ya yi amfani da dubarunsa ya kawar da guguwar ba tare da sanin magoya baya ba, sai dai ka ji kalaman mamaki na fita a bakunansu hakan zai kara sanya kai mai karatu ka sani WAMAKKO BAWAN JAMA'A NE!.