Ramadan: Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Sha’aban
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammd Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan Sha’aban in da ya ayyana yau Lahadi 11 ga watan Fabarairu ta zama 1 ga watan Sha’aban 1445.
Sarkin musulmi y aba da sanarwar ne ga manema labarai a wata takarda da wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin harkokin addini a majalisar sarkin musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu, hakan ke nuna watan Ramadan zai zo nan da kwana 30.
Da yawan musulmi musamman a Nijeriya suna fatar ganin watan Ramadan ya zo cikin saukin rayuwa ganin yadda tsadar rayuwa ke kara ta'azara a kasar abinci ya gagari talaka.
Malaman addini sun fata wa'azi ga masu hali su taimaki talakawa don samun saukin rayuwar yau da kullum.
managarciya