Ramadan: Gwamna Radda zai Raba Abincin Naira biliyan 9 ga Talakawa 

Ramadan: Gwamna Radda zai Raba Abincin Naira biliyan 9 ga Talakawa 

A taron shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar domin shirya wa zaben kananan hukumomi a Katsina, mataimakin gwamnan jihar ya fadi nasarorin gwamnatin Radda. 
Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta samu gagarumin ci gaba a bangarorin lafiya, ilimi, noma, da kuma bunkasa rayuwar al’umma. 
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa ana shirin tallafawa talakawa a watan Ramadan. 
Gwamnatin Katsina ta ce taron ya kara fito da aniyar gwamnatin APC na ci gaba da taimakawa al’ummar jihar domin inganta rayuwarsu. 
Mataimakin Gwamna, Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayi hatsi na Naira biliyan 9 domin rabawa al’ummar jihar a watan Ramadan mai zuwa. 
Hatsin da aka saya ya kunshi gero, dawa, da masara, wanda aka ajiye a wurare daban-daban domin tabbatar da isar su cikin lokaci ga al’umma.