Ramadan: Dasuki ya ware miliyan 100 don rabawa mutanen mazabarsa a Sakkwato

Ramadan: Dasuki ya ware miliyan 100 don rabawa mutanen mazabarsa a Sakkwato
 

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato, Abdussamad Dasuki ya yi abin alheri ga yan yankinsa. 

Hon. Dasuki ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 domin azumin watan Ramadan ga jama’ar mazabarsa da ke jihar Sokoto. 
Dasuki ya mikawa kwamitin mutum 35 domin sayen kayan tallafi da rarraba su, yana mai cewa hakan ya dace da halin tattalin arziki, cewar Tribune. 
'Dan majalisar ya ce yadda Ramadan ya gabato yana bukatar ba al'umma tallafi domin rage musu wahala. 
“Ramadan yana gabatowa, kuma abin da muke yi yau shi ne tabbatar da cewa Musulmai a Kebbe/Tambuwal sun samu tallafi yayin azumin Ramadan." 
“Muna son tabbatar da cewa an rarraba tallafin kafin Ramadan domin rage radadin rayuwa ga jama’a yayin wannan wata mai alfarma." 
Hon. Dasuki ya ce kwamitin agajin Ramadan ya kunshi limamai da shugabanni a mazabar domin tabbatar da cewa kayan tallafin sun isa ga mabukata. 
Kwamitin yana karkashin jagorancin Hon. Abubakar Sadiq Sanyinna, shugaban dattawan Tambuwal, tare da Hon. Adamu Haruna Kebbe a matsayin mataimaki.
Sakataren kwamitin shi ne Hon. Attahiru Danmadi, babban hadimin majalisa ga Hon. Dasuki, tare da shugabannin PDP na Kebbe da Tambuwal a cikin kwamitin. 
Dasuki ya bukaci mutanen mazabar Kebbe/Tambuwal da su rungumi kyautatawa da taimakon juna domin karfafa hadin kai da jin kai a tsakanin al’umma.