PDP Za Ta  Ladabtar Da Wike, Ortom, Makinde Da Sauransu 

PDP Za Ta  Ladabtar Da Wike, Ortom, Makinde Da Sauransu 

PDP Za Ta  Ladabtar Da Wike, Ortom, Makinde Da Sauransu 


Akwai yiyuwar jam’iyyar PDP ta latabtar da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da sauran gwamnonin G5. Rahotanni sun tabbatar cewa jam’iyyar PDP na kokarin shawo kan dukkan matsalolin da jam’iyyar ta fada ciki, Legit.ng ta tattaro. 
Daily Trust ta tattaro cewa PDP na dab da dakatar da shi ko kuma ta kore shi gaba daya daga jam’iyyar. 
“Jam’iyyar PDP na dab da dakatar da Wike ko kararshi gaba daya a jam’iyyar, su na jira ne kawai a rantsar da shi a matsayin minister. 
“Jam’iyyar ta na son bin matakin cikin tsanaki saboda Wike ya na da mutane a jam’iyyar.” 
Majiyar ta ce a kwanakin nan an gano Wike tare da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje watakila ya na shirin koma wa jam’iyyar ce. 
“Kun gan shi ya kai ziyara wurin Ganduje, shugaban APC, watakila ya na son sauya sheka zuwa APC ne ko kuma wannan abu zai sa a kore shi. "Da zarar an rantsar da ministoci, ina mai ba da tabbaci PDP za ta dauki mataki.”