Babban Daraktan Kamfen shugaban kasa a jam’iyar PDP Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa duk wani shiri ya kammala na soma yakeuwar zaben shugaban kasa a 2023 jam’iyarsu da dan takararsu Atiku Abubakar sun shirya tsaf.
Za a kaddamar da yekuwar ne a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a cewar Tambuwal PDP ta shiga gaban sauran jam’iyun adawa in da sun kasa motsawa a ayukkan kamfe.
Ya ce yekuwar su za ta mayar da hankali ne kan abubuwan cigaba za su tallata dan takararsu kan abubuwan da zai kawo.





