PDP za ta fara zawarcin Kwankwaso domin ya sake komawa jam'iyar

PDP za ta fara zawarcin Kwankwaso domin ya sake komawa jam'iyar

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce nan ba da jimawa ba za ta tuntubi tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa kwankwaso, domin ya sake komawa jam'iyyar a yi tafiya tare domin ganin bayan jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Mai riƙon muƙamin shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagun ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam'iyyar, PDP ta mutu, kuma ba za ta iya wata nasara ba a nan gaba.

Ya jaddada cewa a yanzu haka a shirye suke su karbi duk wasu 'ya'yansu da suka yi fushi suka tafi wasu jam'iyyu, ciki har da Sanata Kwankwanson.

''Mutum zai iya faden ra'ayinsa, amma ina so in tuna masa baya, a lokacin da suka bar jam'iyyar PDP a 2015, in ba ta mutu ba a wancan lokacin, a 2015, a lokacin da suke ganin sun yi mata illa to ba n ga dalilin da za a ce ta mutu ba yanzu,'' in ji shugaban.