Home Uncategorized PDP za ta bayar da takarar shugaban ƙasa ga yankin Arewa

PDP za ta bayar da takarar shugaban ƙasa ga yankin Arewa

3
0

Akwai matuƙar tsammanin jam’iyar PDP za ta bayar da takarar shugaban ƙasa a ɓangaren Arewacin Nijeriya a zaɓen 2023 in da za ta kai matsayin shugaban jam’iya a gefen kudu.

A lokacin taron shugabannin jam’iyar a ƙarshen sati sun sanar da cewa za su faɗi yanda karɓa-karɓar za ta kasance a zaman da za a yi ran 9 ga Satumban 2021.

Wannan ya zo ne kan faɗi tashin jagororin siyasar jam’iyar ke yi wanda yakai ga sanya 30 da 31 na Okotoba za a yi babban taron jam’iyar.

Zaɓen shugabannin jam’iyar zai cigaba duk da rigimar shari’ar da ake yi a kotuna.

Yankin Arewa maso Yamma har yanzu bai da zaɓaɓɓin shugabanni tun sanda aka shirya zaɓe bai yiwu ba kan rigimar Tambuwal da Kwankwaso abin jira a gani za a yi zaɓen kafin babban taro ko sai bayan taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here