PDP ta zaftare wata biyu daga cikin wa'adin mulkin Secondus 

PDP ta zaftare wata biyu daga cikin wa'adin mulkin Secondus 
PDP ta zaftare wata biyu daga cikin wa'adin mulkin Secodus 
Jam'iyar PDP ta zaftare wata daga cikin wa'adin mulkin shugabanta Uche Secodus in da zai sauka a watan Oktoba maimakon Disamba da zai kammala wa'adinsa.
Gwamnan Sakkwato kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP Aminu Waziri Tabuwal ne ya karanta jawabin bayan taro ya ce  masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar PDP na ƙasa sun gudanar da zama na musaman a yau Talata a hidikwatar  Jam'iyyar dake Wadata Plaza a birnin tarayya Abuja domin samo baki zaren matsalolin da suka dabaibaye Jam'iyyar.
Ya ce  Bayan doguwar tuntuba ga dukkan bangarorin Jam'iyyar  domin nemo bakin zaren matsalolin da suka dabaibaye Jam'iyyar, wadda ita ce kadai Jam'iyyar da zata iya karawa da Jam'iyyar APC mai mulki kuma ta yi galaba akan ta saboda ta gaza wajen tafiyar da al'amura a kasa baki daya an aminta da abi dokoki. Jam'iyya wajen warware matsalolinta.
"Dole dukkan wasu bangarorin da basa ga-maciji da juna su mayar da takubbansu kube domin cigaban Jam'iyyar PDP da kuma kokarin ceto Najeriya daga halin Ni'yasu da wannan Gwamnati ta Jam'iyyar APC ta jefa ta a ciki.
"Dole abi dukkan wasu hanyoyi da zasu tabbatar da cewar an gudanar da babban taron Jam'iyyar na kasa a watan Oktoba tare da baiwa kowane bangare na Jam'iyyar 'yancin da yake da shi musamman Kwamiton zartarwa na kasa na Jam'iyyar." a cewar Tambuwal.
Ya ce zaman ya buƙaci Kwamitin zartarwar Jam'iyya na kasa da ya gaggauta kafa kwamitin da zai tsara yankunan da shugabannin Jam'iyyar za su fito, da kuma samar da wani kwamiti  daban da zai gudanar da zaɓen shugabannin Jam'iyya.
Rikicin na PDP zai iya lafawa kafin kafa kwamitin zaɓe daga nan a ɗaura in da aka tsaya domin masu son sai shugaba Secodus ya tafi da masu son ya cigaba sun riga sun ja layi har ɓangare guda ya karɓi ragamar jam'iya.
Managarciya na ganin da wahalar gaske rigimar nan ba tai har shekarar 2023 ba ganin dukkan ɓangarorin suna tayar da jijiyar wuya ne domin samun guri a 2023.